Philippians 1

1Wasiƙa daga Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu,

zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya
A alʼadance su bishob
da kuma masu hidima:

2Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi.

Godiya da Adduʼa

3Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4A cikin dukan adduʼoʼina dominku duka, nakan yi adduʼa da farin ciki kullum 5saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yǎ zuwa yanzu, 6da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yǎ zuwa ranar Kiristi Yesu.

7Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina ɗaure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni. 8Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.

9Adduʼata ita ce: ƙaunarku ta yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, 10don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yǎ zuwa ranar Kiristi, 11cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi-zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.

Sarƙoƙin Bulus Sun Sa Ci gaban Bishara

12To, ina so ku sani ʼyanʼuwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara. 13Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada
Ko kuwa dukan fada
da kuma ga kowa cewa an ɗaure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi.
14Saboda sarƙoƙina, yawancin ʼyanʼuwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagaɗi da kuma babu tsoro.

15Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin waʼazin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi. 16Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara. 17Na farin dai suna waʼazin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.
Waɗansu rubuce rubucen hannun da ba su daɗe ba suna da aya 17 kafin aya 16.
18Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki.

I, zan kuwa ci gaba da farin ciki,
19gama na san cewa ta wurin adduʼoʼinku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. 20Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa. 21Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. 22In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! 23Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan: Ina shaʼawa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba; 24amma ya fi muku in rayu cikin jiki. 25Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki, 26domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina. 27Komene ne ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara 28ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku-wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. 29Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, 30da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha.

Copyright information for HauSRK